AUREN MUTU'A HARAMUN NE HAR ZUWA RANAR K'IYAMA!!!
Gabatarwa:
Dukkan yabo da godiya da kirari sun tabbata ga allah, mahaliccin kowa da komai, wanda yake cewa a cikin littafinsa na al-qur'ani:
" allah yana goge abinda yaga dama{ na hukunci} ya tabbatar da abinda yaga dama { na hukunci}" { suratur-ra'adi aya ta 39. tsira da aminci su kara tabbata ga annabin rahma, annabi muhammad da alayensa da sahabbansa da duk wadanda suka bi tafarki irin nasu har zuwa ranar karshe.
Bayan haka:
Hakika wata doguwar tattaunawa ta gudana tsakanina da wasu bayin allah mabiya tafarkin shi'ah masu limamai goma sha biyu, { rafidwawa} a shafin yanar gizo na face book dangane da auren mutu'a. nayi rubutu domin tabbatarda cewa auren mutu'a haramunne a musulunci, sai da yawa daga cikin mabiya wannan tafarki na rafidwawa ma'abota wannan shafin sukayo ca akaina cewa karya kawai na rubuta, domin kuwa gashi a malamammu na sunnah an samo wadanda suka goyi bayan auren mutu'a a littatafansu musamman a wajen fassarar ayannan ta 24 a cikin suratun-nisa'i. Daga cikin malamanda suka kawo sunansu akwai:
1.al-imam a'dabariy
2.az-zamakhshariy
3.ar-raziy
4.imam ahmad
5.aljassas
6.albaiha'kiy
7.albaidawiy
8.ibn katheer
9.as-shaukaniy
10.al-alusy da sauransu.
Wannan tasa dani da sauran 'yan uwa muka tashi mukai rubutu me tsayi me gamsarwa dangane da bayanin wa'dannan 'karerayi da suka yiwa wa'dannan malamai ta hanyar kawo duk maganganun malamanda suka ambata kai tsaye daga cikin littatafansu domin al'umma suga irin 'karya da tadlisin 'yan shi'a [ rafidawa}.
To bayan tsawon lokaci da yin wannan rubutu muna karatun littafin sharhus-sunnah na imam albarbahariy a masallacin juma'a na sheikh jibril umar jibril dake triumph fagge sai karatu ya biyo ta kan auren mutu'a, sai na kawo maganganun malamai akan cewa haramunne tare da 'karfafar maganganun da hadisan manzon allah sallal-lahu alaihi wa aalihi wa sallam, bayan mun gama karatu sai wani dan uwa yai min tambaya cewa ya zamuyi da ayarda su 'yan shi'a suke kafa hujja da ita a cikin suratun-nisa'I ? domin ya karanta wani littafi nasu sun kawo maganganu cewa malamai a ciki hadda wasu daga sahabbai sunce ayar nan tana magana halacci auren mutu'a. sai na bashi amsa a ta'kaice saboda 'karancin lokaci, amma nai masa al'kawari cewa zan lalubo masa wannan rubutun da muka gabatar a shafin yanar gizo na face book domin 'kara tattara bayanai da dalilai. Bayan sati mun dawo gurin karatu sai na bashi takardun da zimmar yayi kwafi ya dawo min da asalin, munyi haka ranar talata, allah cikin ikonsa ranar alhamis naje wani shago domin nayi kwafin wasu takardu sai daya daga cikin 'yan uwa wato kabiru kamba yake nuna mini har sun maida wa'dannan takardu dana basu suyi kwafi littafi domin kwa'dayin suma su ya'dashi cikin al-umma su sami lada. Wannan tasa suka birgeni ni kuma nace su bani naje na 'kara wasu abubuwan a inda ake bu'katar 'kari din na cire abinda ba bu'katar barinsa.
A karshe ina rokon allah ta'ala daya sakawa dukkan wanda yake da hannu wajen wannan rubutu da ya'duwarsa a cikin al'umma da alkhairi, yasa kuma kar'ba'bbene wannan aikin a gurinsa, sannan ya sakawa malamammu da alkhairi ya gafartawa wa'danda suka rasu a cikinsu saboda 'dawainiyarda sukai damu ta karantarwa babu dare babu rana, musamman marigayi sheikh abubakar hussaini albany fagge da sheikh ja'afar mahmood adam da sauransu.
Anas muhammad assalafiy fagge
Lahadi 4/11/1435 a.h _28/8/2014 a.d
Ma'anar auren mutu'a:
Imam az-zar'kaniy ya fassara auren mutu'a a cikin littafin sharhuz-zar'kaniy ala muwa'dda'I malikin {3/197} da cewa: " auren mutu'a shine wani aure na dan wani lokaci".
Haka nan as-sheikh ahmad abul-barakat ad-dardeer a cikin littafin as-sharhul-kabeer {2/3} ya fassarashi da cewa: "………ha'ki'kanin mutu'arda ake rabata har abada itace ayi daurin aure tare da ambatawa waliyyin mace ko ita ajalin auren…".
Haka nan abul-hasan al-mardawiy a cikin littafin al-insaf {8/163} ya fassara shi da cewa: " auren mutu'a shine {mutum} ya aureta {mace} zuwa wani dan lokaci".
Sheikhul-islam ibn taimiyya ya fada kamar yadda yazo a almuharrar {2/23} yace: " duk wanda ya auri mace zuwa wani dan lokaci to shine auren mutu'a".
Ga dukkan wanda ya karanta wadannan ma'anoni da malamai suka rubuta ze fahimci auren mutu'a aurene da ake yinsa da niyya ko sanin ma'auratan cewa zuwa wani lokaci sananne aure ya mutu base an ambaci saki ba, da zarar wannan lokacin yayi shike nan.
Tarihin auren mutu'a:
Ibnul-arabiy almalikiy yana fada kamar yadda imam az-zar'kaniy ya kawo a sharhinsa na muwadda {3/199}: " auren mutu'a yana cikin abubuwanda suke daban{baki} a cikin shari'ar musulunci, an halatta shi sannan aka haramta shi, sai aka 'kara halatta shi, sannan aka 'kara haramta shi, halattawar farko saboda yayi shiru akansa a farkon musulunci sai mutane suka ci gaba da aikata shi bisa al'adarsu {ta larabawa a jahiliyya}, sannan aka haramta shi ranar ya'kin khaibar, sannan aka halattashi ranar ya'kin audas da fathu makka a bisa hadisin jabir {r.a} da waninsa, sannan aka sake haramta shi haramci na har abada a dai ita ranar fathu makka saboda hadisin saburata {r.a}".
Imam muhammad bn ahmad al'kurdubiy yake fada a cikin tafsirinsa na aljami'I {3/18}: " amma mutu'ar mata tana cikin abubuwanda suke daban {ba'ki} a musulunci, saboda an halattata a farkon musulunci sannan aka haramta ranar ya'kin khaibar, sai aka sake halattawa ranar ya'kin au'das daga nan aka sake haramtawa, al-amarin ya tabbata akan haramci….".
Idan muka lura da wadannan bayanai na malamai akan tarihin auren mutu'a zamu fahimci cewa da halal ne kuma daga baya wanda ya halatta ya haramtashi har abada. Kuma sannan zamu ga cewa halattawanda akayi matsalace tasa saboda sahabbai sun tsinci kansu a cikin tsanani a wajen ya'ki, kamar yadda ze bayyana a cikin dalilai nan gaba da yardar allah.
Magan-ganun malaman musulunci akan auren mutu'a:
Imam as-shafi'iy ya fada a cikin littafinsa al'um bugu na biyu darul-ma'rifa {5/11}: " auren mutu'a be halatta ba, kuma za'a rabasa {idan anyi} kuma kadai mun haramta mutu'ane saboda biyayyar sunnah……"
Imam addardir abul-barakat yake fada a cikin littafin as-sharhul-kabeer {2/3} : " auren mutu'a ana raba shi {idan anyi} ba tare da saki ba, kuma ana yiwa ma'auratan biyu u'kuba abisa mazhaba, a wata fadar akace za ai musu haddi ne [ba u'kuba ba}".
Imam muhammad bn abiy sahal as-sarkhasiy almabsud {5/152}: " bayani ya iskemu daga manzon allah alaihis-salatu was-salam cewa ya halatta mutu'a tsawon kwana uku a wani zamani a wani ya'ki da akai gwauranta tayiwa {sahabbai} tsanani, sannan {daga baya} yai hani da shi {mutu'ar}"
Imam abul-hasan almalikiy a cikin littafin kifayatud-dalibir-ra bbaniy, sharhin risala{2/67} yace: " haka ma auren mutu'a be halatta ba da ijma'in malamai…."
Imam al-khaddabiy a cikin ma'alimus-sunan {3/190} yake cewa: " auren mutu'a akwai sa'bani akansa a zamanin farko, amma daga baya dukkan al-umma sunyi ijma'I akan haramcinsa har zuwa ranar 'kiyama. Babu wanda ya saba wannan ijma'in se mutanenda ba'a la'akari da sabaninsu, wato sune rafida 'yan bid'a".
Wadannan sune kadan daga cikin magan-ganun malamai akan auren mutu'a, wanda suke nuni cewa malaman musulunci gaba daya sun tafi akan haramcin auren mutu'a ada da yanzu kamar yadda ibn rushud ya fada a cikin bidayatul-mujtahid {2/48} cewa: "ammma auren mutu'a duk malaman garuruwa{duniya} sun hadu akan haramcinsa".
Dalilan haramcin auren mutu'a:
•على بن أبى طالب رضى الله عنه : أن رسول الله -صلى الله عليه وسلم- نهى عن متعة النساء يوم خيبر وعن أكل لحوم الحمر الإنسية.
AN RUWAITO DAGA ALIYU (RA); LALLAI MANZON ALLAH (SAW) YA YI HANI AKAN MUTU'A DA MATA A RANAR YAK'IN KHAIBARA, DA CIN NAMAN JAKUNAN GIDA.
BUKHARI DA MUSLIM.
•عن الحسن وعبد الله ابنى محمد بن على عن أبيهما : أن عليا رضى الله عنه قيل له إن ابن عباس رضى الله عنهما لا يرى بمتعة النساء بأسا. فقال : إن رسول الله -صلى الله عليه وسلم- نهى عنها يوم خيبر وعن لحوم الحمر الإنسية.
AN RUWAITO DAGA HASSAN DA ABDULLAHI 'YA'YAN MUH'D 'DAN ALIYU DAGA BABANSU YA CE; LALLAI ALIYU (RA) AN CE MASA; GA IBNU ABBAS (RA) YANA GANIN BABU LAIFI AKAN MUTU'A DA MATA. SAI YA CE: LALLAI MANZON ALLAH (SAW) YA YI HANI AKANTA (MUTU'A DA MATA) A RANAR YAK'IN KHAIBARA, DA CIN NAMAN JAKUNAN GIDA.
BUKHARI DA MUSLIM.
•سالم بن عبد الله : أن رجلا سأل عبد الله بن عمر رضى الله عنهما عن المتعة فقال : حرام قال فإن فلانا يقول فيها فقال : والله لقد علم أن رسول الله -صلى الله عليه وسلم- حرمها يوم خيبر وما كنا مسافحين.
AN RUWAITO DAGA SALIM 'DAN ABDILLAHI; WANI MUTUM YA TAMBAYI ABDALLAHI 'DAN UMAR (RA) GAME DA MUTU'A, SAI YA CE: HARAMUN NE. SAI YA CE: AI WANE YANA FA'DIN HALACCINTA. SAI YA CE: NA RANTSE DA ALLAH YA SANI CEWA; MANZON ALLAH (SAW) YA HARAMTATA A RANAR YAK'IN KHAIBARA, DON HAKA MU BA MASU HARKA DA DADURO BA NE (KARUWAI).
DUBA SUNANUL KUBARA NA AL-BAIHAK'IY , A BABIN AUREN MUTU'A.
•عن الربيع بن سبرة الجهنى عن أبيه سبرة رضى الله عنه أنه قال : أذن رسول الله -صلى الله عليه وسلم- بالمتعة فانطلقت أنا ورجل إلى امرأة من بنى عامر كأنها بكرة عيطاء فعرضنا عليها أنفسنا فقالت : ما تعطينى فقلت : ردائى وقال صاحبى : ردائى وكان رداء صاحبى أجود من ردائى وكنت أشب منه فإذا نظرت إلى رداء صاحبى أعجبها وإذا نظرت إلى أعجبتها ثم قالت : أنت ورداؤك تكفينى فكنت معها ثلاثا ثم إن رسول الله -صلى الله عليه وسلم- قال :« من كان عنده شىء من هذه النساء التى يتمتع بهن فليخل سبيلها ».
AN RUWAITO DAGA RABE'U 'DAN SABURA AL-JUHANIY DAGA BABANSA SABURA (RA) YA CE; MANZON ALLAH (SAW) YA YI IZNIN MUTU'A, SAI NA TAFI NI DA WANI MUTUM ZUWA WAJEN WATA MATA DAGA BANI AMIR, KAI KA CE DAK'WALWAR BUDURWA CE, SAI MUKA NUNA MATA KANMU, SAI TA CE; ME ZAKU BANI, SAI NA CE: MAYAFINA, SAI ABOKINA YA CE: MAYAFINA. AMMA MAYAFIN ABOKIN NAWA YA FI NAWA KYAU, AMMA NI NA FI SHI SAMARTAKA. TO IDAN TA DUBA MAYAFIN ABOKINA SAI YA BIRGETA, IDAN KUMA TA DUBENI SAI IN BIRGETA, SAI TA CE MINI: KAI DA MAYAFINKA KUN ISHENI, SAI NA ZAUNA TARE DA ITA TSAWON KWANA 3. SA'ANNAN SAI MANZON ALLAH YA CE: DUK WANDA AKWAI IRIN WA'DANNAN MATA DA YAKE MUTU'A DASU, TO YA RABU DA ITA.
MUSLIM.
•الربيع بن سبرة عن أبيه عن جده قال : أمرنا رسول الله -صلى الله عليه وسلم- بالمتعة عام الفتح حين دخلنا مكة ثم لم نخرج منها حتى نهانا عنه.
DAGA SABURA (RA) YA CE: MANZON ALLAH (SAW) YA UMURCEMU DA MUTU'A A SHEKARAR FATHU MAKKA A LOKACIN DA MUKA SHIGA MAKKAN, SA'ANNAN BA MU FITA DAGA MAKKAN BA HAR SAI DA YA HANAMU GAME DA MUTU'AN.
DUBA SUNANUL KUBURA NA AL-BAIHAK'IY , A BABIN AUREN MUTU'A.
•الربيع بن سبرة عن أبيه : أن رسول الله -صلى الله عليه وسلم- نهى عن المتعة وقال :« إنها حرام من يومكم هذا إلى يوم القيامة ومن كان أعطى شيئا فلا يأخذه ».
DAGA SABURA (RA); LALLAI MANZON ALLAH (SAW) YA HANAMU MUTU'A, KUMA YA CE: TA HARAMTA DAGA YAU HAR RANAR K'IYAMA. DUK WANDA YA BA DA WANI ABU TO KAR YA KAR'BA.
MUSLIM
•الربيع بن سبرة عن أبيه رضى الله عنه قال : رأيت رسول الله -صلى الله عليه وسلم- قائما بين الركن والباب وهو يقول :« يا أيها الناس إنى كنت أذنت لكم فى الاستمتاع ألا وإن الله حرمها إلى يوم القيامة فمن كان عنده منهن شىء فليخل سبيلها ولا تأخذوا مما آتيتموهن شيئا ».
DAGA SABURA (RA) YA CE: NA GA MANZON ALLAH (SAW) YANA TSAYE A TSAKANIN RUKUNI (HAJARUL ASWAD) DA KOFAN KA'ABA, YANA CEWA: YA KU MUTANE! LALLAI NA YI MUKU IZNIN MUTU'A, TO KU SAURARA KU JI; LALLAI ALLAH YA HARAMTATA HAR ZUWA RANAR K'IYAMA, TO DUK WANDA YAKE TARE DA WATA MACE TA MUTU'A, TO YA RABU DA ITA, KUMA KAR KU KAR'BI WANI ABU DA KUKA BASU.
MUSLIM.
•عن إياس بن سلمة بن الأكوع عن أبيه رضى الله عنه قال : رخص رسول الله -صلى الله عليه وسلم- فى متعة النساء عام أوطاس ثلاثة أيام ثم نهى عنها بعد.
DAGA IYAS BIN SALAMA BIN AL-AKWA'A, DAGA BABANSA (RA) YA CE: MANZON ALLAH (SAW) YA YI RANGWAME GAME DA MUTU'AR MATA A SHEKARAR YAK'IN AU'DAS, TSAWON KWANA 3, SA'ANNAN YA YI HANI AKAI DAGA BAYA.
MUSLIM.
•عن أبى جمرة قال سمعت ابن عباس وسئل عن متعة النساء فرخص فيها فقال له مولى له : إنما كان ذاك وفى النساء قلة والحال شديد ، فقال ابن عباس : نعم.
DAGA ABU JAMRA YA CE: NA JI IBNU ABBAS AN TAMBAYE SHI GAME DA MUTU'AR MATA, SAI YA YI RANGWAME AKAI, SAI WANI MAULANSA YA CE MASA: AN YI RANGWAME AKAN HAKAN NE A LOKACIN MATA 'YAN KA'DAN NE, KUMA ANA YANAYI NA TSANANI. SAI IBNU YA CE: EH, HAKA NE.
BUKHARI.
• عن أبى ذر قال : إنما أحلت لنا أصحاب رسول الله -صلى الله عليه وسلم- متعة النساء ثلاثة أيام ثم نهى عنها رسول الله -صلى الله عليه وسلم
AN RUWAITO DAGA ABU ZARR (RA) YA CE: MU SAHABBAN MANZON ALLAH (SAW) KAWAI AN HALASTA MANA MUTU'A DA MATA NE, TSAWON KWANA 3, SA'ANNAN SAI MANZON ALLAH (SAW) YA YI HANI AKANTA.
DUBA SUNANUL KUBURA NA AL-BAIHAK'IY , A BABIN AUREN MUTU'A
Wadannan sune dalilai daga manzon allah alaihis-salatu was-salam da suke nuna da auren mutu'a halal ne saboda wata maslaha, sai daga baya allah mai girma da buwaya ya haramta shi har abada. Don haka duk wanda yayi auren mutu'a yanzu ya sabawa allah da manzon allah, allah ya kiyashe mu.
Auren mutu'a a gurin rafidawa {'yan shi'a}:
Duk da wadannan dalilai da suka nuna mana haramcin auren mutu'a a fili 'kiri-'kiri amma su rafidawa 'yan shi'a suka kauda idanunsu suka halarta shi suka sanya masa falala sama da aure na sharia dawwamamme !! kamar yadda hakan yazo a littatafansu da dama. Ga kadan Daga cikin abinda suke cewa:
Babban malamin shi'a al-majlisi a cikin littafinsa biharul-anwar {100/319-320} yana cewa: " ya halatta ayi mutu'a da mata karuwai da wadanda suka shahara da fajirci".
Haka malaminsu mulla alkashaniy a cikin littafinsa manhajus-sadi'kina {356} yace: " hakika dan matarda akai mutu'a da ita yafi danda akai dawwamammen aure" !!
Tsokaci:
Ga duk mai hankali wadannan ruwayar tana nuna cewa 'ya'yansu na mutu'a sunfi manzon allah ! domin manzon allah alaihis-salatu was-salam ta hanyar aure dawwamamme aka same shi !! wal'iyazu billah !!!
Haka nan babban jagoransu muhammad bn ya'akub alkulainiy a cikin littafin furu'ul-kafiy {5/462} yace: " auren mutu'a da mata kyawawa ya halatta koda matar aure ce ko karuwa".
Tsokaci:
Ga duk mai hankali idan ya kalli wannan ruwayar ta shi'a ze fahimci nufinsu kawai shine yada zinace-zinace hatta da matan aure !! allah ya tsare mu.
Duk da wadannan ruwayoyi nasu za'a iya samun wani dan shi'an yace ai malamansu na wannan zamanin basa goyon bayan wadannan ruwayoyi. To ga magana jagoransu na wannan zamanin:
Khumaini a cikin littafin tahrirul-wasiila {2/256} yake cewa: " ya halatta za'a iya mutu'a da mazinaciya amma akwai karhanci idan ta shahara da zinar".
To 'yan uwa wannan shine matsayin auren mutu'a a wajen 'yan shi'a. allah ya tsaremu sharrin son zuciya.
Shubuharda shi'a suke fakewa da ita akan mutu'a:
'yan shi'a suna kawo shubuha da sunan kafa hujja akan auren mutu'a, suna fakewa da ayar nan ta cikin suratun-nisa' aya ta 24, dai dai inda allah yake cewa:
فما استمتعتم به منهن فآتوهن أجورهن فريضة ولا جناح عليكم فيما تراضيتم به من بعد الفريضة إن الله كان عليما حكيما
Ma'ana: "…..duk wadanda kukaji dadi dasu {mata} ku basu ladansu {na sadaki} farilla ne, babu laifi akanku ga abinda kukai yarjejeniya dashi bayan farilla {sadaki}, lallai allah ya kasance masani mai hikima". Wannan itace ayarda shi'a suke kafa hujja da ita wajen mutu'a. kuma abinda ya rudesu a cikin ayar shine kalmar:
فما استمتعتم به منهن فآتوهن أجورهن فريضة
Wannan ayar tasa suka ringa yiwa malaman tafsiri karya duk sun fassara ayar da ma'anar auren mutu'a wannan kalmar take nufi. Daga ciki suna kawo sunayen malamada na kawo a baya.
Wanda kuma duk malamannan babu wanda ya goyi da bayan fassararsu kamar yadda zamu gani a fasali na gaba da yardar allah.
Raddi akan shubuhar 'yan shi'a akan mutu'a:
.hakika malaman musulunci sunyi raddi akan ma'anarda shi'a suke bawa wannan aya ta 24 a cikin suratun-nisa'I, babu 'daya daya goyi da bayan fassararsu.
Fadin allah {s.w.t} ::
فما استمتعتم به منهن فآتوهن أجورهن فريضة ولا جناح عليكم فيما تراضيتم به من بعد الفريضة إن الله كان عليما حكيما.
Fassararda imam ad-dabariy ya yiwa ayar:
1- WANNAR AYA ITA CE HUJJAR RAFIDA WAJEN HALASTA MUTU'A. TO A WAJEN TAFSIRINTA 'DABARIY YA AMBACI FASSARA GUDA 2;
• AYAR TANA MAGANA NE AKAN AUREN HALAL.
• AYAR TANA MAGANA NE AKAN AURE MUTU'A.
DUKANSU 'DABARIY YA AMBACESU A WAJEN TAFSIRIN AYAR.
TO WANNE DADAI??
SAI AL-'DABARIY (R) YA CE:
قال أبو جعفر: وأولى التأويلين في ذلك بالصواب، تأويل من تأوله: فما نكحتموه منهن فجامعتموه، فآتوهن أجورهن = لقيام الحجة بتحريم الله متعة النساء على غير وجه النكاح الصحيح أو الملك الصحيح على لسان رسوله صلى الله عليه وسلم.
MA'ANA: YA CE: FASSARA MAFI DACEWA DA DADAI, ITA CE FASSARAR WANDA YA FASSARA DA CEWA; ABIN DA KUKA AURA NA MATA SA'ANNAN KUKA SADU DA SU, TO KU BA SU SADAK'INSU. SABODA HUJJA TA TSAYA DAGA BAKIN MANZON ALLAH (SAW) BISA HARAMCIN YIN MUTU'A DA MATA, BA TA FISKAR INGANTACCEN AURE BA, KO INGANTACCEN MALLAKAR BAIWA.
DAGA NAN SAI YA RUWAITO HADISI DA YAKE NUNA CEWA; MA'ANAR FA'DIN ALLAH:
''فماستمتعتم''
NA CIKIN AYAR INGANTACCEN AURE YA KE NUFI, BA AUREN MUTU'A BA.
الربيع بن سبرة الجهني، عن أبيه: أن النبي صلى الله عليه وسلم قال: استمتعوا من هذه النساء = والاستمتاع عندنا يومئذ التزويج.
DAGA RABE'U BIN SABURAH AL-JUHANIY DAGA BABANSA; LALLAI MANZON ALLAH (SAW) YA CE: KU JI DA'DI DA WA'DANNAN MATAN. JIN DA'DI DA MATA A WAJENMU A WANNAN LOKACI SHI NE; AURE
.
MAGANAR CEWA WASU DAGA CIKIN SAHABBAI SUN KARANTA AYAR DA K'ARIN;
الى اجل مسمى.
LALLAI SHI 'DABARIY YA YI RADDINTA, YA CE:
وأما ما روي عن أبي بن كعب وابن عباس من قراءتهما:( فما استمتعتم به منهن إلى أجل مسمى ) ، فقراءة بخلاف ما جاءت به مصاحف المسلمين. وغير جائز لأحد أن يلحق في كتاب الله تعالى شيئا لم يأت به الخبر القاطع العذر عمن لا يجوز خلافه.
MA'ANA; AMMA ABIN DA AKA RUWAITO DAGA UBAYYI 'DAN KA'AB DA IBNI ABBAS CEWA; SUNA KARANTAWA; ZUWA LOKACI AMBATACCE (SANANNE), KARATU NE DA YA SA'BA MA ABIN DA YA ZO CIKIN LITTAFIN K'UR'ANIN MUSULMAI. BA YA HALATTA GA WANI YA KAWO WANI ABU YA HA'DA DA AYA A CIKIN LITTAFIN ALLAH, WANDA BABU HADISI TABBATACCE MAI YANKE UZURI, DAGA ABIN DA BA HALATTA A SA'BA MASA BA.
TO JAMA'A KUN GA DAI YADDA 'DABARIY YA YI RADDIN WANNAN K'IRA'A SHAZZA TA SU UBAYYI DA IBNU ABBAS (RA). DON HAKA DUK WANDA YA CE: 'DABARY YA K'ARFAFA CEWA; AYAR TA SAUKA NE AKAN AUREN MUTU'A, TO YA YI K'ARYA.
Maganar az-zamakhshariy akan ayar:
AL- ZAMAKHSHARIY DUK DA CEWA MU'UTAZILI NE, GA MAGANARSA A WAJEN TAFSIRIN AYAR:
(فما استمتعتم به منهن) فما استمتعتم به من المنكوحات من جماع أو خلوة صحيحة أو عقد عليهن.
MA'ANA; ABIN DA KUKA JI DA'DI DA SHI NA ABIN AURE, NA JIMA'I, KO INGANTACCE KE'BEWA, KO 'DAURIN AURE.
SAI KUMA YA AMBACI 'DAYA FASSARAR;:
وقيل نزلت في المتعة التى كانت ثلاثة أيام حين فتح الله مكة على رسوله عليه الصلاة والسلام ثم نسخت كان الرجل ينكح المراة وقتا معلوما ليلة أو ليلتين أو أسبوعا بثوب أو غير ذلك ويقضي منها وطره ثم يسرحها سميت متعة لاستمتاعه بها أو لتمتيعه لها بما يعطيها
وعن عمر لا اوتى برجل تزوج امرأة إلى اجل الا رجمتهما بالحجارة
وعن النبي ( صلى الله عليه وسلم ) أنه أباحها ثم أصبح يقول
268 ( يا ايها الناس إني كنت أمرتكم بالاستمتاع من هذه النساء الا ان الله حرم ذلك إلى يوم القيامة )
وقيل أبيح مرتين وحرم مرتين
وعن ابن عباس هي محكمة يعني لم تنسخ وكان يقرأ ( فما استمتعتم به منهن إلى اجل مسمى ) ويروى انه رجع عن ذلك عند موته وقال اللهم إني أتوب اليك من قولي بالمتعة وقولي في الصرف
النساء
YA CE; KUMA AN CE; WAI AYAR TA SAUKA NE AKAN MUTU'AR DA TA KASANCE TSAWON KWANA 3, A LOKACIN FATHU MAKKA, SA'ANNAN SAI AKA SHAFE MUTU'AR. …
SA'ANNAN SAI YA KAWO CEWA; UMAR (RA) YA YI GARGA'DI AKAI. SAI YA KAWO HADISI; MANZON ALLAH (SAW) YA HALATTA MUTU'A, SA'ANNAN SAI YA CE: YA KU MUTANE, NA UMURCEKU DA JIN DA'DI DA WA'DANNAN MATAN, SAI DAI ALLAH YA HARAMTA HAR ZUWA RANAR K'IYAMA''.
TO KA GA KENAN BABU MAI CEWA; UMAR (RA) NE YA HARAMTA SAI JAHILI KO MAI SON RAI.
SA'ANNAN SAI YA CE; AN RUWAITO DAGA IBNU ABBAS (RA) CEWA; HUKUNCIN AYAR YANA NAN, KUMA HAR YANA KARANTAWA DA:
الى اجل مسمى.
SAI DAI ANA RUWAITOWA DAGA GARE SHI CEWA; YA DAWO DAGA WANNAR FAHIMTA LOKACIN MUTUWARSA, YA CE: YA ALLAH INA TUBA GAREKA GAME DA RA'AYINA NA MUTU'A, DA NA SARF.
TO KA GA ZAMAKHSHARIY KO KA'DAN BAI 'DAURE WA MUTU'A GINDI BA. BA WANDA ZAI FAHIMCI HAKA SAI MAI SON RAI. KUMA YA BAYYANA CEWA IBNU ABBAS YA DAWO YA BAR K'IRA'ARSA YA TUBA MA ALLAH. .
Maganarda ake cewa nawawiy yayi wanda asalinta maganar al-maziriy ce, cewa:
وتعلقوا بقوله تعالى فما استمتعتم به منهن فآتوهن أجورهن وفي قراءة بن مسعود فما استمتعتم به منهن إلى أجل وقراءة بن مسعود هذه شاذة لا يحتج بها قرآنا ولا خبرا ولا يلزم العمل بها.
MA'ANA; Rafida sun ma'kalewa fadin Allah:
A 'kira'ar dan mas'ud da 'karin :فما استمتعتم به منهن فآتوهن أجورهن );
Wannan 'kira'a ta ibn mas'ud shazzace ba'a kafa hujja da ita a 'kur'anance ko a hadisi. Kuma ba'a lazimta aiki da ita.الى اجل. .
Maganar imamu ahmad akan ayar:
Maganar cewa imamu ahmad ya karfafi cewa ayar tana magana ne akan mutu'a a cikin musnad nasa ba dai-dai bace, domin idan ka zakace ya fadi abu dole ya zamto maganarsa ce ba ruwayar maganar wani yayi ba. in kuma akwai inda ya 'karfafi maganar da ra'ayinsa sai a kawo gurin.
MU DAI GA ABIN DA MUKA SANI DAGA IMAMU AHMAD GAME DA AUREN MUTU'A; YA CE A RISALARSA ZUWA GA MUSADDaD BIN MUSARHAD:
ولا نكاح إلا بولي وخاطب وشاهدي عدل والمتعة حرام إلى يوم القيامة.
Babu aure seda waliyyi da mai nema da shedu biyu adalai, auren mutu'a kuma haramunne har zuwa ranar 'kiyama".
{'daba'katul-hanabil a, babin musaddad. 1/343}
Maganar al-jassas akan ayar:
AMMA SHI AL- JASSAS CEWA YA YI:
وأما احتجاج من احتج فيها بقوله تعالى فما استمتعتم به منهن فآتوهن أجورهن وأن في قراءة أبي إلى أجل مسمى فإنه لا يجوز إثبات الأجل في التلاوة عند أحد من المسلمين فالأجل إذا غير ثابت في القرآن ولو كان فيه ذكر الأجل لما دل أيضا على متعة النساء لأن الأجل يجوز أن يكون داخلا على المهر فيكون تقديره فما دخلتم به منهن بمهر إلى أجل مسمى فآتوهن مهورهن عند حلول الأجل
YA CE: AMMA WANDA YA KAFA HUJJA DA WANNAR AYAR, SABODA A K'IRA'AR UBAYYI (RA) AKWAI;
الى اجل مسمى.
Bai halatta a wajen wani daga cikin musulmai ya tabbatarda kalmar ajalin a karatu, don haka 'karin ajalin bai tabbata ba a cikin 'kur'ani, kuma koda akwai ambaton kalmar ajalin duk da haka baya nuni akan mutu'a da mata. Domin ajalin ya halatta zai iya shiga cikin maganar sadaki, sai ta'kdirin ya zamo: duk wadanda kuka tare dasu daga ciki akan sharadin sadaki sai wani ajali sananne to ku basu sadakinsu idan ajalin ya cika..
KUMA DU YA Ce:
وفي فحوى الآية من الدلالة على أن المراد النكاح دون المتعة ثلاثة أوجه.
A CIKIN MA'ANAR AYAR, AKWAI DALILI AKAN CEWA; ANA NUFIN AURE NE BA MUTU'A BA, TA FISKOKI GUDA 3:
SAI YA AMBACESU.
KUMA DU YA CE:
ولما كانت هذه المعاني موجودة في المتعة كانت في معنى الزنا ويشبه أن يكون من سماها سفاحا ذهب إلى هذا المعنى.
YA CE: SABODA SAMUN WA'DANNAN MA'ANONI A CIKIN MUTU'A, TO TA KASANCE KAMAR ZINA NE. TA YIWU SABODA WANNAN MA'ANA NE, WANDA YA KIRA MUTU'A DA SUNAN KARUWANCI, YA KIRATA DA HAKAN.
KUMA DU YA CE:
وقد روي عن جماعة من السلف أنها زنا
YA CE: HAK'IK'A AN RUWAITO DAGA MAGABATA MASU YAWA, SUNA CEWA; MUTU'A ZINA Ce.
Maganar albaiha'kiy akan auren mutu'a:.
AMMA SHI BAIHAK'IY: AMMA SHI AL-BAIHAK'IY GA DUKKAN MAGANGANUN DA YA YI A BABIN MUTU'A. SAI A NUNA MANA INDA YA K'ARFAFA MAGANAR MUTU'AR:
قال الشافعى ذكر ابن مسعود الإرخاص فى نكاح المتعة ولم يوقت شيئا يدل أهو قبل خيبر أو بعدها وأشبه حديث على بن أبى طالب رضى الله عنه فى نهى النبى -صلى الله عليه وسلم- عن المتعة أن يكون والله أعلم ناسخا له.
YA CE: IMAMU SHAFI'IY YA CE: IBNU MAS'UD (RA) YA AMBACI RANGWAME GAME DA MUTU'A, AMMA BAI FA'DI WANI LOKACI DA ZAI NUNA CEWA; SHIN KAFIN YAK'IN KHAIBARA NE KO BAYANSA. AMMA TA YIWU HADISIN ALIYU (RA) NA HANIN ANNABI (SAW) AKAN MUTU'A YA KASANCE YA SHAFE RANGWAME AKAN MUTU'A DAKE CIKIN HADISIN IBNU MAS'UD (RA).
KUMA DU YA CE:
قال الشيخ رحمه الله : وهذا الذى قاله سفيان محتمل فلولا معرفة على بن أبى طالب رضى الله عنه بنسخ نكاح المتعة وأن النهى عنه كان البتة بعد الرخصة لما أنكر به على ابن عباس رضى الله عنهما والله أعلم وروى عن ابن عمر تحريمها يوم خيبر.
YA CE: ABIN DA SUFYANU('DAN UYAINA) YA FA'DA ANAN ABIN DUBAWA NE. SABODA BA DON ALIYU (RA) YA SAN AN SHAFE HALASCIN MUTU'A BA, KUMA HANI AKAI YA KASANCE NE BAYAN RANGWAME BA, DA BAI YI INKARI WA IBNU ABBAS (RA) BA. KUMA AN RUWAITO HADISIN HARAMCIN MUTU'AR A RANAR YAK'IN KHAIBARA DAGA ABDULLAHI 'DAN UMAR (RA).
KUMA DU YA CE:
قال الشيخ ثم إن رسول الله -صلى الله عليه وسلم- أذن فى نكاح المتعة زمن الفتح فتح مكة ثم حرمها إلى يوم القيامة وذلك بين فيما أخبرنا أبو طاهر الفقيه
YA CE: SA'ANNAN MANZON ALLAH (SAW) YA YI IZNIN MUTU'A A LOKACIN FATHU MAKKA, SA'ANNAN YA HARAMTATA HAR ZUWA RANAR K'IYAMA.
KUMA DU YA CE:
فقد نقل نهيه عنها بعد الإذن فيها ولم يثبت الإذن فيها بعد غزوة أوطاس فبقى تحريمها إلى الأبد والله أعلم
YA CE: HAK'IK'A AN RUWAITO HANI AKAN MUTU'A BAYAN AN YI IZNI AKANTA, IZNI AKAN MUTU'A BAI TABBATA BA BAYAN YAK'IN AU'DAAS, DON HAKA SAI HARAMCIN YA TABBATA HAR ABADA.
KUMA DU YA CE:
قال الشيخ : ونحن لا نشك فى كونهما على عهد رسول الله -صلى الله عليه وسلم- لكنا وجدناه نهى عن نكاح المتعة عام الفتح بعد الإذن فيه ثم لم نجده أذن فيه بعد النهى عنه حتى مضى لسبيله -صلى الله عليه وسلم- فكان نهى عمر بن الخطاب رضى الله عنه عن نكاح المتعة موافقا لسنة رسول الله -صلى الله عليه وسلم- فأخذنا به
YA CE: BA MA SHAKKA CEWA; MUTU'A 2, NA MATA DA NA HAJJI, SUN KASANCE A ZAMANIN MANZON ALLAH (SAW), SAI DAI MUN SAMU YA YI HANI AKAN MUTU'AR MATA A SHEKARAR FATHU MAKKA BAYAN YA YI IZNI AKAI, SA'ANNAN BA MU SAMU YA YI IZNI AKAI BA BAYAN YA YI HANIN, HAR UMAR (RA) YA BI TAFARKINSA . HANIN UMAR (RA) GAME DA MUTU'A YA DACE DA SUNNAR MANZON ALLAH (SAW), SAI MUKA YI RIK'O DA SHI.
Maganar al-baidawiy akan ayar:
AL- BAIDAWIY:
وقيل نزلت الآية في المتعة التي كانت ثلاثة أيام حين فتحت مكة ثم نسخت لما روي أنه ( صلى الله عليه وسلم ) أباحها ثم أصبح يقول يا أيها الناس إني كنت أمرتكم بالاستمتاع من هذه النساء ألا أن الله حرم ذلك إلى يوم القيامة وهي النكاح المؤقت بوقت معلوم سمي بها إذ الغرض منه مجرد الاستمتاع بالمرأة أو تمتيعها بما تعطي وجوزها ابن عباس رضي الله عنهما ثم رجع عنه
YA CE: AN CE; WAI WANNAR AYAR TA SAUKA NE AKAN MUTU'A DA TA KASANCE TA KWANA 3, LOKACIN FATHU MAKKA, SA'ANNAN SAI AKA SHAFE HALASCINTA, SABODA ABIN DA AKA RUWAITO; MANZON ALLAH (SAW) YA HALASTA, SAI YA WAYI GARI YANA CEWA: YA KU MUTANE; LALLAI NA UMURCEKU DA JIN DA'DI DA WA'DANNAN MATAN, KU SAURARA KU JI!! LALLAI ALLAH YA HARAMTA HAKAN HAR ZUWA RANAR K'IYAMA''.
SHI NE; AUREN 'DAN LOKACI SANANNE. AN KIRA SHI DA WANNAN SUNA NE (MUTU'A) DON MANUFARSA KAWAI; JIN DA'DIN MACE, KO KUMA DA'DA'DA MATA DA ABIN DA ZA A BATA. IBNU ABBAS (RA) YA HALASTA SA'ANNAN YA DAWO DAGA HALASCIN.
Maganar ibn katheer akan ayar:
IBNU KASEER:
وقد استدل بعموم هذه الآية على نكاح المتعة، ولا شك أنه كان مشروعا في ابتداء الإسلام، ثم نسخ بعد ذلك.
YA CE: WASU SUN KAFA HUJJA DA GAMAYYAR WANNAR AYAR AKAN HALASCIN MUTU'A, AMMA BABU SHAKKA YA KASANCE AN SHAR'ANTA SHI A FARKON MUSLUNCI, SA'ANNAN SAI AKA SHAFE HALASCIN DAGA BAYA.
Bayanin as-shaukaniy akan mutu'a
AL- SHAUKANIY:
وقد قال بجوازها جماعة من الروافض ولا اعتبار بأقوالهم وقد أتعب نفسه بعض المتأخرين بتكثير الكلام على هذه المسألة وتقوية ما قاله المجوزون لها وليس هذا المقام مقام بيان بطلان كلامه
وقد طولنا البحث ودفعنا الشبه الباطلة التي تمسك بها المجوزون لها في شرحنا للمنتقى
YA CE: WASU MUTANE RAFIDA SUN CE MUTU'A HALAL NE, AMMA BA A DAMUWA DA MAGANGANUNSU. HAK'IK'A WANI DAGA CIKIN 'YAN BAYA YA WAHALAR DA KANSA WAJEN YAWAITA MAGANA AKAN WANNAR MAS'ALAR DA K'ARFAFA RA'AYIN MASU HALASTAWA, AMMA NAN BA WAJEN YI MASA RADDI BA NE. HAK'IK'A MUN TSAWAITA BAHASI, MUN YI RADDIN DUKKAN 'BATATTUN SHUBUHOHIN MASU HALASTAWA A CIKIN SHARHIN ''AL-MUNTAK'A'' WATO ''NAILUL AU'DAAR''.
Maganar al-alusiy akan ayar:
AL- ALUSIY:
والقول بأنها نزلت في المتعة غلط وتفسير البعض لها بذلك غير مقبول لأن نظم القرآن الكريم يأباه
YA CE: RA'AYIN CEWA; AYAR NAN TA SAUKA NE AKAN MUTU'A MUMMUNAN KUSKURE NE, KUMA FASSARAR DA WASU SUKE YI MA AYAR DA MUTU'A, SAM BA KAR'BA'B'BE BA NE, DON SIYAK'IN K'UR'ANIN BA ZAI KAR'BE SHI BA.
KUMA DU YA CE:
قوله عز من قائل : فإذا استمتعتم وهو يدل على أن المراد بالاستمتاع هو الوطء والدخول لا الاستمتاع بمعنى المتعة التي يقول بها الشيعة والقراءة التي ينقلونها عمن تقدم من الصحابة شاذة
YA CE; FA'DIN ALLAH MABUWAYI, IDAN KUN JI DA'DI, YANA NUNI NE AKAN ABIN DA AKE NUFI DA JIN DA'DIN SHI NE SADUWA TA AURE DA SHIGA DA MATA BAYAN AURE. BA YANA NUFIN JIN DA'DI NA MUTU'A BA NE, WANDA 'YAN SHI'A SUKE FA'DI, KUMA K'IRA'AR DA SUKE RUWAITOWA DAGA SAHABBAI SHAZZIYA CE. (MA'ANA; TA SA'BA MA INGANTACCIYAR K'IRA'A)
Maganar rasheed rida akan ayar:
RASHEED RIDA:
وذهبت الشيعة إلى أن المراد بالآية " نكاح المتعة " : وهو نكاح المرأة إلى أجل معين كيوم أو أسبوع أو شهر مثلا ، واستدلوا على ذلك بقراءة شاذة رويت عن أبي ، وابن مسعود ، وابن عباس رضي الله عنهم وبالأخبار والآثار التي رويت في المتعة ، فأما القراءة فهي شاذة لم تثبت قرآنا ، وقد تقدم أن ما صحت فيه الرواية من مثل هذا آحادا ، فالزيادة فيه من قبيل التفسير ، وهو فهم لصاحبه ، وفهم الصحابي ليس حجة في الدين ، لا سيما إذا كان النظم والأسلوب يأباه كما هنا ، فإن المتمتع بالنكاح الموقت لا يقصد الإحصان دون المسافحة ، بل يكون قصده الأول المسافحة.
YA CE: 'YAN SHI SUN TAFI AKAN CEWA; MA'ANAR AYAR ''AUREN MUTU'A'' NE, …. KUMA SUN KAFA HUJJA NE DA K'IRA'A SHAZZIYA (MA'ANA; TA SA'BA MA INGANTACCIYAR K'IRA'A) WACCE AKA RUWAITO DAGA UBAYYI, IBNU MAS'UD, IBNU ABBAS (RA), DA KUMA HADISAI DA ATHAR DA AKA RUWAITO AKAN MUTU'A. AMMA ITA K'IRA'A SHAZZIYA CE, BA TA TABBATA K'UR'ANI BA. IRIN WANNAN IN TA TABBATA TO RUWAYA CE KA'DAITACCIYA, (WACCE BA TA TA'BA ZAMA K'UR'ANI, SABODA SHI DOLE SAI RUWAYA TA ZAMA MUTAWATIRA), KAWAI IN AN SAMU K'ARIN TAFSEERI CE, KUMA FAHIMTAR SAHABI SHI KA'DAI (WANDA YA SA'BA MA SAURAN SAHABBAI) BA YA ZAMA HUJJA A ADDINI. MUSAMMAN MA IN SIYAK'IN K'UR'ANI DA USLUBINSA BAI DACE DA SHI BA. LALLAI MAI YIN MUTU'A BA YANA NUFIN KARE KANSA NE BA, KAWAI YANA NUFIN KARUWANCI NE, KAI ASALI MA TUN FARKO MANUFARSA ITA CE; KARUWANCI.
KUMA DU YA CE:
والحاصل أن القرآن بعيد من هذا القول ، ولا دليل في هذه الآية ولا شبه دليل عليه ألبتة .
YA CE: SAKAMAKON BAYANIN NAN; LALLAI K'UR'ANI YA YI NESA DA WANNAN RA'AYI (FASSARA AYAR DA MUTU'A), BABU WANI DALILI A CIKIN AYAR KAI KO KAMA DA DALILI AKAN RA'AYIN BABU, KWATA – KWATA.
KUMA DU YA CE:
ويرى أهل السنة أن الرخصة في المتعة مرة أو مرتين يقرب من التدريج في منع الزنا منعا باتا كما وقع التدريج في تحريم الخمر ، وكلتا الفاحشتين كانت فاشية في الجاهلية
YA CE: RA'AYIN AHLUS SUNNA SHI NE; RANGWAMEN DA AKA YI AKAN MUTU'A SAU 1, KO SAU 2, YA YI KAMA DA MATAKAI WAJEN HANA ZINA HANAWA NA GABA 'DAYA, KAMAR YADDA HAKAN YA FARU WAJEN HARAMTA GIYA, SABODA DUKKAN ALFASHA GUDA 2, SUN WATSU A ZAMANIN JAHILIYYA.
SUYU'DIY KUMA A CIKIN DURRUL MANTHUR, RUWAYOYI YA TARA KAWAI BA SHI RA'AYI KO 'DAYA CIKIN LITTAFIN SHI YASA YAKE CIKE DA HADISAI MASU RAUNI, HAR DA NA K'ARYA. SHI YA SA RAFIDA SUKA YAWAITA KWASO KOWANE IRIN HADISI DAGA CIKINSA.
Ya 'yan uwa wadannan sune malamanda 'yan shi'a rafidawa sukewa 'karya wai sun goyi da bayan auren mutu'a. gashi mun kawowa me karatu magan-ganunsu gaba daya babu wanda bai 'karyata zancen na 'yan shi'a ba, kuma sun tabbatar mana da cewa ruwayoyi da ake kawowa daga dan abbas da dan mas'ud da ubayyu allah ya 'kara musu yarda baki 'dayansu 'kira'ace shazza ba mutawatira ba, don haka ba'a aiki da ita
.
DON HAKA LALLAI WANNAR AYAR BABU DALILI GA WANDA YA HALATTA MUTU'A A CIK.
DA MA SHI AUREN MUTU'A YA TABBATA NE A HADISI BA A K'UR'ANI BA. SABODA A FARKON MUSLUNCI BUK'ATA TA SA MANZON ALLAH (SAW) YA HALALTA MUSU MUTU'A, AMMA DAGA BAYA YA HANA YIN MUTU'AR YA HARAMTA TA HAR ZUWA RANAR K'IYAMA, DON HAKA SAYYIDINA UMAR (RA) MA A ZAMANINSA YA K'ARFAFA HARAMCIN DA MANZON ALLAH (SAW) YA YI.
JAMA'A MUN DAI FAHIMCI CEWA RAFIDA BA SU DA WANI DALILI NA ALK'UR'ANI AKAN MUTU'A, SAI K'IRA'A SHAZZA (MA'ANA; TA SA'BA MA INGANTACCIYAR K'IRA'A). SABODA HAKA DUK WANDA YA CE; AKWAI DALILI A CIKIN K'UR'ANI AKAN MUTU'A, YA ZAMA CIKAKKEN MAK'ARYACI, SABODA JAHILCI, KO SON ZUCIYA DA SON RAI.
* DUK WANDA YA YI AUREN MUTU'A A YANZU, YA ZAMA CIKAKKEN MAZINACI!!!
Wannan shine 'karshen wannan rubutu, muna rokon allah ta'ala ya karba mana baki daya ya kuma nuna mana gaskiya gaskiyace ya bamu ikon binta, ya nuna mana 'karya 'karyace ya bamu ikon guje mata.
Tsira da aminci su 'kara tabbata ga shugaban farko da 'karshe, da alayensa da sahabbansa da wadanda sukabi tafarkinsu har zuwa ranar 'kiyama……..